
Na’urar masu tan-tance masu zaɓe ta gaza karbar hannun ɗan takarar jami’uyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar, Eyitayo Jegede.
Ɗan takarar shi da matar sa sai da suka shafe mintina biyar bisa kin gane hannun na su da na’urar ta yi.
Hakan shi ne lokaci na farko da na’urar ta gaza tantancewa tun fara zaɓen.
Sai dai diyar tankarar gwamnan ta samu damar yin zabe tun da wuri.