Zaɓen Ondo: ‘Ina da Ƙwarin gwiwar Samun Nasara’ – Jegede

0
123

Ɗan takarar jami’iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar Ondo da yake gudana yanzu haka, Eyitayo Jegede ya ce yana da tabbacin samun nasara a zaben na jihar Ondo.

Jegede ya zanta da ‘yan jaridu jim kadan bayan kada kuri’ar a akwatin zabe dake Firamaren Sacred Heart a Akure.

Jegede wanda ya yi tsayuwar mintuna 30 kafin na’urar tantance masu zabe(Card reader ta tantance shi ya bayyana rashin gamsuwa da ra yadda na’aurar ke aiki.

Ya bukaci hukumar zabe ta INEC da ta kara kokari wajen sanya na’urar ta dinga aiki yadda yakamata don bawa masu kada kuri’a damar yin zabe.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here