Zaɓen Ondo: Gwamna Akeredolu Na Jam’iyyar APC na Kan Gaba a Sakamakon Farko Dake Fitowa

0
158

Rotimi Akeredolu, gwamnan jihar Ondo kuma dan takarar jami’iyyar APC a zaben da aka gudanar yau 10 ga watan Oktoba, ya na kan gaba da tazarar kuri’u 35, 000.

Kamar yadda sakamakon zaben da hukumar zabe ta INEC ta wallafa a cibiyoyin tattara sakamakon zabe na kananan hukumomi bakwai, Akeredolu ya samu kuri’u 97_625 yayin da Eyitayo Jegede na PDP ke biye masa da kuri’u 62, 435.

Sai Agbola Ajayi na ZLP wanda yake na uku da kuri’u 19, 132.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here