Zaɓen Ondo: Ɗan takarar Jami’iyyar APC, Akeredolu Ya Kaɗa Kuri’ar Sa

0
163

Dan takarar gwamna na jami’iyyar APC, Rotimi Akeredolu, ya kada kuri’ar sa

Ya isa rumfar zabe ta 6, mazaba ta 5 dake Isokub a yankin Ijebu Owo dake Jihar.

Gwamnan wanda yake sanye da farar kaya ya isa rumfar zaben da misalin karfe 9:37 na safe bayan daukewar ruwan sama da aka fara tun safe.

Bai tsaya bin layi ba kai tsaye yaje wajen tantance masu zabe tare da matar sa.

Yayin da yake magana da yan Jaridu, Akeredolu wanda ke neman sake darewa karagar mulki karo na 2 ya ce Allah ne zai bashi nasara.

Akeredolu ya ce, “Ina da kwarin gwiwar samun nasarar zaben nan.”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here