An yi Kira da A Samu Haɗin Kai Tsakanin Hukumomin Tsaro da Kafafen Yaɗa Labarai Wajen Shawo Kan Matsalar Tsaro

0
244

Hukumomin tsaro, Wakilan kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki sun amince su yi aiki tare don yaƙi da ta’addanci da sauran matsalolin rashin tsaro.

Jami’an tsaron tare da ƴan Jarida sun amince cewa dole a samu fahimtar juna tsakanin hukumomin tsaro da ƴan jarida don tabbatar da an yaɗa sahihan bayani da za su taimaka wajen rage ayyukan masu aikata laifuffuka da kuma bunkasa kokarin jami’an tsaro na dakile ayyukan yan bindiga da sauran laifuka.

Hakan na ɗauke ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban kungiyar wakilan kafafen yaɗa labarai ta kungiyar ƴan jaridu ta kasa reshen jihar Kano, Malam Ibrahim Garba Shuaibu da Manajan Cibiyar PRNigeria, na Kano, Adnan Mukhtar Adamu da aka fitar jim kadan bayan kammala bada horo na kwana daya kan “Aikin Jarida na Kafar sadarwa ta zamani da Tsaron Kasa: Rawar da masu fada aji za su taka wajen yaƙi da aikata laifuka”, wanda cibiyar ta PRNigeria ta shirya yau a Kano.

Samarwar ta kuma yi nuni da cewa, ana tsammanin sashin hulɗa da jama’a na hukumomin tsaro za su yi aiki tare da wakilan kafafen yaɗa labarai a bamgaren samar da tsare-tsare, gamsassun bayanai kan kokarin hukumomin tsaro na yaƙi da ayyukan ƴan bindiga, ƴan tada kayar baya da sauran masu aikata laifuffuka.

Yayin tattaunawa a taron, mahalarta taron da suka haɗa da wakilan hukumomin tsaro daban-daban, shugabannin kafafen yada labarai, ƴan jarida da sauran masu ruwa da tsaki sun amince kan cewa halin tsaro da ake ciki a Najeriya da alaqar dake tsakanin kafafen yaɗa labarai da hukumomin tsaro na bukatar a bunkasa ta.

Sanarwa ta ce “matsalar rashin tsaro da ake fuskanta a Najeriya musamman a yankin arewacin Najeriya abin dubawa ne, abin damuwa inda suka yi kira da a ɗauki matakan da suka dace.

“Dole ne ayi wannan yunkuri don dakile matsalar tsaro. Kamar akwai rashin jituwa tsakanin hukumomin gwamnati, musamman jami’an dake kula da lamarin. Akwai rashin alaqa ta kusa tsakanin masu magana da yawun hukumomi da kafafen yaɗa labarai da suka hada da masu fada aji”.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, ” wasu masu magana da yawun hukumomin har yanzu basu lura da muhimmancin kafafen sadarwa na zamani wajen kula da fannin tsaro ba. Samuwar kafafen sadarwa na zamai ya zama abu mai sauki wajen wasu masu amfani da ita wajen yada kalaman batanci da labaran karya.

Sanarwa ta kuma yi nuni da cewa, Kyakkwawan shugabanci da bin doka da Oda shi ne zai zama mabuɗin gyara.

Rashin motsawa wajen kawo karshen matsalar tsaro musamman ta hanyar wayar da kai.

Sanarwa ta kuma yi bayanin cewa akwai bukatar kafawa, gudanarwa tare da bunƙasa alaƙar dake tsakanin hukumomi don tattara bayanan sirri tare fa aiki tare wajen yaki da masu aikata laifuka.

Sanarwa ta jaddada cewa, karfafa alaqar dake tsakaninn wakilan kafafen yada labarai wajen tabbatar da samar da bayanai a kan lokaci zai ci gaba da dorewa.

Taron bada horan ya kuma yi nuni da bukatar , yin duk abinda ke yuwuwa wajen kawo karshen rikici ta hanyar shirye-shirye da dama”.

Sanarwa ta kuma kara da cewa akwai bukatar tafiya tare da matasan Najeriya wajen tabbatar da cewa sun yi amfani da kafafen sadarwa na zamani ta hanyar da yakamata musamman rubutun da suke wallafawa ya mayar da hankali wajen gina kasa da samun kwanciyar hankali.

Haka kuma sama da mutane 30 daga hukumomin tsaro, Kafafen yada labarai, Kungiyoyi, malaman makaranga da kungiyoyin matasa ne suka halarci taron bada horan.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here