Zaben Ondo: Jigo a APC Ya Nemi Kotu Ta Soke Chan-Chantar Gwamna Akeredolu na Shiga Zaben

0
131

Wani Jigo a jam’iyyar APC ya bukaci babbar kotun tarayya dake Abuja da ta soke chan-chantar Gwamna Rotimi Akeredolu na jam’iyyar APC daga shiga zaben gwamnan jihar da za’ayi gobe.

Mai ƙarar ya yi zargin cewa gwamnan ya zama ɗan takarar jami’iyyar APC ba bisa ƙa’ida ba.

Barista Kalu Kalu Agu, wanda ya shigar da ƙarar a yau Juma’a ƙasa da awanni 24 a gudanar da zaben, ya yi iƙirarin cewa kasancewar Akeredolu a masatiyin ɗan takara ya saɓawa doka kasancewar babu shugaban jami’iyya ko Sakatare ya yin da aka yi zaben fidda gwani.

Barista Agu, ya kuma kalubalanci rushe kwamitin tafikar da jami’iyyar karkashin jagorancin Adams Oshiomhole da kwamitin zababbun jami’iyyar ya yi ƙarƙashin jagorancin shugaba Buhari a ranar 25 ga watan Yuni.

Ya kuma nemi Kotun da ta cire duk wani dan takara daga jami’iyyar APC daga shiga zabe har sai an kammala sauraran ƙarar dake kalubalantar rushe shugabancin jami’iyyar ƙarƙashin Adams Oshiomhole.

 

Sai dai kotun ba ta sanya ranar sauraran ƙarar ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here