Facebook Ya ƙi sanya Tallar Albasa Mai Kama da Tsiraicin Mata – BBC

0
348

 

Sashin Hausa na BBC ya wallafa Rahotan cewa, Akwai albasa irin wacce aka saba gani, sannan akwai wacce Facebook ke ganin yanayinta bai dace a sanya a shafin ba saboda tana kama da siffar jikin mata, kamar yadda wani kamfanin samar da irin kayan noma na Canada ya gano a baya-bayan nan.

Kamfanin na EW Gaze da keSt John’s a Newfoundland, ya so ya sanya tallar wani irin albasa ta Walla Walla a Facebook.

Sun yi mamakin yadda aka ƙi karɓar tallar saboda cewa abin ya yi kama da ”tsiraici”.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, kamfanin Facebook ya bayar da haƙuri kan kuskuren wani saƙo da na’urar kamfanin ta wallafa.

Tallar da aka sanya a Facebook ɗin ta nuna albasar Walla Walla, wacce aka san ta da girma da zaƙi, an zuba ta a cikin kwando sannan da wata da aka yanka an ajiye ta daga gefe.

Manajan kamfanin albasar, Jackson McLean ya ɗauki lokaci kafin ya gano matsalar saƙon da ake magana akai wanda aka wallafa ɗin, in ji kamfanin.

Daga nan sai ya gano cewa akwai matsala game da siffar albasar, wadda ta yi kama da nonuwa da mazaunai.

1px transparent line

Ya san cewa abokan hulɗarsa za su mayar da batun ƙin karɓar tallar abin dariya, sai ya wallafa hoton tare da saƙon da na’urar Facebook ɗin ta aika musu na ƙin sanya tallar don su gani su tabbatar

Mr McLean ya ce wasu abokan hulɗar sun yi ta wallafa hotuna na karas da kabewa da wasu irin yanayin daban yayin da suke tsokaci.

Ya kuma ɗaukaka batun matakin ga Facebook.

”Muna amfani da na’ura wajen tantance duk wani abu da aka turo na batsa don ta kawar da shi, amma wani lokacin ba lallai ta fahimci wasu abubuwan kamar albasar Walla Walla ba,” kamar yadda shugaban yaɗa labarai na kamfanin Facebook na Canada Meg Sinclair, ya shaida wa BBC.

“Mun dawo sake sa tallar kuma muna ba da haƙuri kan abin da hakan ya jawo.”

Mr McLean ya ce kamfanin yana mayar da komai intanet ne don sauƙaƙa wa masu sayayya a lokacin annobar cutar korona, kuma hakan ya haɗa da ƙara yin talla kamar ta wannan albasar a Facebook.

“Mun sayar da albasa da dama cikin kwana uku da suka gabata fiye da wacce muka sayar cikin shekara biyar da suka wauce,” a cewar Mr McLean, yana mai cewa a yanzu an saka su a jerin ”albasa masu siffsar jikin mata” a shafin intanet na kamfanin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here