Da Yuwuwar Tattalin Arzikin Najeriya Ya Ƙara Samun Koma Baya – Buhari

0
211

Da yuwuwar Tattalin Arzikin Najeriya ya ƙara samun koma baya a shekara huɗu tare da samun mummunan sakamako inji shugaban ƙasa Buhari.

Buhari ya faɗi hakanne yayin gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2021 a zaman haɗin gwiwa na majalisun kasar nan.

Kasafin kuɗin dai an sanya shi a Naira Tiriliyan 13.08 da farashin gangar ɗanyen mai kan Dala 40 da kuma fitar ganga Miliyan 1.86 kowacce rana.

Yayin da yake gabatar da ƙunshin kasafin, shugaban ƙasa Buhari ya ce kasafin kudin na 2021 an shirya shi ne a daidai lokacin da duniya ke fuskantar kalubalen da annobar Korona ta haifar, karyewar farashin danyen mai da matsalar tattalin arziki a fadin duniya.

Tattalin arzikin Najeriya dai a yanzu yana fuskantar kalubale, inji shi tare da illar da annoba ta yiwa tattalin arzikin kasa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here