Za’a Koma Dukkan Makarantu a Birnin Tarayya Abuja Ranar Litinin – Minista

0
148

Ministan babban birnin tarayya Abuja, ya bada umarni ga dukkan makarantu a Abuja da su koma karatu a ranar 12 ga watan Oktoba da muke ciki.

A wata sanarwa da aka fitar a daren yau Alhamis mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun ministan, Anthony Ogunleye, Mista Bello ya ce za’a fitar da ka’idojin da aka shimfiɗa na sake buɗe makarantun nan bada jimawa ba.

Ya ce, birnin tarayya Abuja bai samu bullar cutar Korona ba yayin da aka bude makarantu ga yan ajin karshe.Ya kuma bukaci mahukunta da ɗalibai su bi ka’idojin kariya daga cutar Koroma yayin da aka buɗe karatun.

Ita ma shugabar kwamitin komawa makarantu ta birnin tarayya Abuja, Fatima Abdulrahman, ta ce ɗalibai “za su yi amfani da satin farko na komawa makarantar wajen yin bita sai mako na biyu da za su zana jarrabawar zangon karatu na biyu wanda aka dakatar bayan bullar annobar Korona”.

Jihohi da dama dai sun sanar da ranakun komawa makarantu wadanda suka hada da Kano, Lagos, Oyo da Enugu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here