Yau Za’a Fara Bada Takardar Izinin Shiga Kasar Dubai ga ‘Yan Najeriya

0
84

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa za ta fara bayar da takardar izinin shiga ƙasarta wato bisa ga ƴan Najeriya daga yau Alhamis takwas ga watan Oktoban wannan shekarar.

Bayanan hakan sun fito ne daga bakin ministan sufurin jiragen sama na ƙasa Hadi Sirika, wanda ya ce Haɗaɗɗiyar Daular Larabawan ce ta rubuto wa Najeriyar cewa ta amince a bayar da takardar bisa ɗin ga ƴan ƙasar amma kuma a bisa wasu ka’idoji.

Hukukamar shige da fice ta kasa ta jaddada wa masu aniyar tafiya ƙasar da su bi dokokin don kaucewa tsatsauran hukunci.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here