Yaki da Cin Hanci da Rashawa Ya Kawo Karshen Harkallar Zamba Cikin Aminci ta Filaye a Jihar Kano – Muhyi Magaji

0
223

Shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado,  a yau Alhamis a Kano ya ce,  yaki da cin hanci da rashawa a jihar ya kai ga samun nasarar kakkabe masu harkallar zanba cikin aminci na filaye da sauran laifuka a jihar.

Barista Muhyi Magaji ya bayyana hakanne yayin bikin ranar masu binciken laifukan almundahana ta duniya na hukumar da hadin gwiwa da hukumar karbar korafe-korafe da hukumar kare hakkin dan ‘adam ta kasa wanda ya gudana a dakin taro na makarantar horarwa na hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano dake Goron dutse.

Ya ce yayin da ya zama shugaban hukumar, ya gaji matsaloli da dama da suka dangancin harkallar filaye ba bisa ka’ida ba tare da warware matsalolin da suka danganci ‘yan kasauwar da suka rasa shagunan su a Kasuwar Kantin Kwari da Kofar wambai inda hukumar ta samu nasarar shawo kan matsalolin su ta hanyar bayan tattaunawa da yan kasuwa sama da dubu biyar.

“Mun kuma taimakawa masu rauni da suka zo gun mu da matsalolin su wajen samar mu su da adalci tare da dawo da hakkin wadanda aka cuta ta hanyar wannan kokarin miliyoyin mutane an biya su ga wadanda suka rasa kwarin gwiwar dawowar kudaden su daga hannun yan damfara”.

Yayin da yake yabawa kokarin masu binciken laifukan almundahana, ya ce duniya ta yadda da tsarin kuma dukkan mutumin da bazai iya daukar lauya ba don kare shi zai iya zuwa wajen masu binciken laifukan kuma a shirye suke wajen dawo da hakkin kowa .

Muhyi ya ce masu binciken sun taimakawa wajen tabbatar da gaskiya a tsarin tafikarwar gwamnati wanda hakan yasa hukumar ta ke da damar shiga kowacce ma’aikata ta gwamnati don tattara bayanai.

“Inda hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ke aiki ba a cin zarafi ko tsoratarwa”.

Shima ana sa bangaren, daya daga cikin mahalarta taron, Dr. DJ Usman ya bibiyi tarihin tsarin masu binciken manyan laifuka a makalar da ya gabatar.

Daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da hukumar EFCC, ICPC da kungiyar lauyoyi ta kasa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here