Kwalejin Ilimi ta Tarayya dake Garin Bichi Ta Yabawa Dan Majalisa Abubakar Kabir Bisa Tallafin Karatu Ga Daliban Yankin

0
91

Kwalejin Ilimi ta Tarayya dake garin Bichi ta yabawa dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Bichi, Abubakar Kabir Abubakar bisa biyan kudi Naira Miliyan 16, 874, 996, 55 a matsayin kudin makaranta ga daliban karamar hukumar dake karatu a kwalejin.

Sakon yabawar yana dauke ne cikin wasikar jinjina mai kwanan wata 8 ga watan Satumba na wannan shekarar kuma mai dauke da sa hannun shugaban kwalejin, Farfesa Bashir Muhammad Fagge.

Wasikar ta ce: “Cikin shekara daya a matsayin wakilin karamar hukumar Bichi a majalisar wakilai ta kase, wannan kwaleji ta shaida gudunmawar da ka bayar ta Naira Miliyan 16, 874, 996, 55 ga dalibai yan asalin karamar hukumar Bichi a shekarar karatu ta 2019/2020.

“Yayin da muke taya ka murna bisa gudunmawar da kake bawa mazabar ka wajen ganin ci gaban ta a fannin raya al’umma, muna addu’ar Allah ya ci gaba da yi ma Albarka da karin damarmaki da ingantacciyar rayuwa.”

Biyan kudin yana daga cikin na dalibai sama da dubu da dan majalisar ya dau nauyin su a mabanbanta makarantu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here