Jami’iyyar PDP ta ce Ba za ta Amince da Ogunbode a matsayin Baturen Zaben Ondo Ba

0
87

Jami’iyyar PDP taki amincewa da zabin mataimakin shugaban jami’ar Obafemi Awolawo, Ile Ife, Farfesa Eyitope Ogunbode, a matsayin babban Baturen zabe a zaben gwamna da za’ayi a jihar Ondo ranar Asabar.

Shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar na PDP, kuma gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ne ya fadi hakan a taron manema labarai da ya gudana yau a birnin Akure na jihar.

Makinde ya ce Ogubbodede dan asalin karamar hukumar Owo ne wacce gwamna Akeredolu dan takarar jami’iyyar APC ya fito.

Sannan ya yi zargin cewa mataimakin shugaban jami’ar magoyin bayan Akeredolu ne kuna bazai yi adalci ba.

Duk da hukumar Zabe ta INEC ba ta sanar da sunan Oginbodede ba, Makinde ya ce an sanar da jami’iyyar cewa an zabe shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here