Gwamnatin Tarayya Ta Fitar da Sabbin Matakan Komawa Makarantu

0
100

Gwamnatin tarayya ta fitar da sabbin matakan sake komawa makarantu a fadin kasarnan.

Dr. Sani Aliyu, babban jami’in tsare-tsare na kwamitin kar ta kwana na fadar shugaban kasa kan yaki da annobar Korona ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai yau Alhamis.

Ya ce, Bangarori da dama da suka hada da damar da makarantu suke da shi na dakatar da yaduwar cutar da kuma tsare-tsaren sadarwa domin yada bayanai kan cutar ta COVID-19, dole ne a lura da su kafin bayar da dama a sake bude makarantun.

“Makarantu da cibiyoyin karatu da suke shirin budewa, dole ne su samu matakan sadarwa wadanda suka hadar da iyaye, tawagar lafiya ta makaranta, hukumomin makaranta da jami’an gwamnatin jiha”, inji shi.

“Sannan dole ne su samar da wani tsari da zai dinga bayar da sabbin bayanai ga iyaye, ma’aikata da hukumomi da kuma hanyoyin sadarwa”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here