Zaben Ondo: APC Ta Nada Sha’aban Sharada a Matsayin Mai Kula da Fannin Tsaro na Kwamitin Yakin Neman Zaben ta

0
179

Kwamitin yakin neman zaben kujerar gwamnan jihar Ondo na jami’iyyar APC, ya nada Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar birni, Sha’aban Ibrahim Sharada a matsayin babban mai kula da fannin tsaro da tafikarwa a zaben jihar da za’a gudanar.

A wata wasika mai kwanan wata, 3 ga Satumba, 2020 mai dauke da sa hannun Sakataren kwamitin, Mustapja Salihu ta ce:

“A madadin shugaban kwamitin yakin neman zaben gwaman jihar Ondo, Babajide Sanwo-Olu gwamnan jihar Legas. Ina farin cikin sanar da kai nada ka a matsayin mai kula da fannin tsaro a babban zaben da za’ayi a jihar Ondo .

A matsayin ka na daya daga cikin shugabannin wannan jami’iyya, kwarewar ka zai zama mai amfani wajen samun nasarar kwamitin da kuma samun nasarar jami’iyyar a zaben gwamnan jihar Ondo dake tafe, “.

Sha’aban Sharada dai shine tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan Rediyo da Talabijin.

Sannan an zabe shi a matsayin dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar birni a shekarar 2019.

Kuma shi ne shugaban kwamitin tsaro da bayanan sirri na majalisar wakilai ta kasa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here