Yanzu-Yanzu: El-Rufai Ya Nada Sabon Sarkin Zazzau

0
124

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya sanar da Magajin Garin Zazzau, Alhaji Ahamd Nuhu Bamalli, a matsayin Sarkin Zazzau na 19 kwanaki 17 bayan rasuwar Sarkin Zazzau na 18, Alhaji Shehu Idris.

Ahamd Nuhu Bamalli dai ya fito ne daga gidan Mallamawa kuma shine tsohon Jakadan Najeriya a kasar Thailand.

An dai haifi shi ne a ranar 8 ga watan Yuni na shekarar 1966 a garin Zaria, mahaifin sa Nuhu Bamalli ya rike Sarautar Magajin Garin Zazzau kafin ya gaje shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here