
Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Kananan hukumomi na kasa(NULGE), Comrade Ibrahim Khalil ya rasu.
Comrade Ibrahim Khalee wanda kuma shi ne ma’ajin kungiyar kwadago ta kasa ya rasu ne a yau Laraba a babban asibitin kasa dake Abuja.
Shugaban kungiyar ta NULGE reshen jihar Kano, Abdullahi Muhammad Gwarzo ne ya tabbatar da mutuwar ta sa a daren yau, inda ya ce za’ayi jana’izar mamacin a karamar hukumar Wudil gobe da yamma dake jihar Kano.