Sabon Sarkin Zazzau Ya Isa Fadar Sa

0
159

Daruruwan masoya da masu fatan Alkhairi sun yi dafifi a fadar Sarkin Zazzau a yau Laraba don nuna goyan bayan su ga sabon Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli.

Bamalli ya isa fadar ne a farar mota kirar BMW inda jama’a da dama suka taru suna murna.

Sabon Sarkin wanda ya sanya farar Babbar Riga da farin takalmi na sarauta, sannan ya fito daga motar ya nufi cikin al’umma.

Masu rike da masarautun gargajiya da dama ne suka yi dafifi wajen nuna mubaya’a ga sabon sarkin.

A yau ne dai gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da nadin Ahamd Bamalli a matsayin Sabon Sarkin Zazzau bayan shafe kwanaki 17 da rasuwar Shehu Idris, Sarki na 18 a masarautar Zazzau.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here