Milyoyin ƴan Najeriya na cikin matsanancin talauci – Osinbajo

0
140

 

Sashin Hausa na BBC Ya wallafa labarin cewa, Mataimakin shugaban ƙasa , Yemi Osinbajo ya yarda cewa milyoyin ƴan ƙasarnan na cikin matsanancin talauci.

Ya ce zaɓaɓɓun shugabanni zai kasance ba su da amfani idan ba su hada kai wajen shawo kan matsalolin da ke barazana ga rayuwar ƴan ƙasar.

Osinbajo ya shaida hakan ne a wani taron kwana biyu kan shugabanci da ake gudanarwa a fadar gwamnati da ke Abuja.

Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma shaida cewa akwai bukatar bangaren majalisa da zartarwa su yi aiki tare muddin ba sa son su gaza a idon ƴan ƙasar da suka zaɓo su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here