Kamfanin Apple Zai Fitar Da Sabuwar Wayar Iphone 12

0
227

Kamfanin Apple ya sanar da ranar fitar da sabuwar wayar Iphone 12.

Kamfanin zai nuna wayar a bikin kaddamar da ita ranar 13 ga watan nan na Octoba, da karfe 10 na safe kamar yadda sanarwar gayyata ta nuna.

Kamar yadda aka saba, wayoyin kamfanin Apple ana sanya su domin siyarwa a cikin kwana 10 don siyarwa bayan an fitar da su wanda hakan yake nuni da cewa za’a fitar da wayar ranar 23 ga watan Oktoba. Sai dai wannan shekarar kamfanin ya sauya jadawalin da ya saba fitar da ita.

Sabuwar wayar ta Iphone dai tana dauke da karfin Network na 5G, kuma ana saran kamfanin zai saki nau’i hudu na wayar ta IPhone 12.

Haka kuma kamfanin Apple zai yi amfani da taron wanda za’a yi ta kafar sadarwa wajen bayyana sababbin abubuwan da ya samar da suka hada da Headphone na Airpods da sauran su.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here