Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa Ta Kama Matashi da Katunan Cirar Kudi a Kano

0
153

Hukumar Hana Fasa Kwauri ta kasa Reshen Jihar kano da Jigawa,  ta ce ta Samu nasarar kams wani matashi mai suna Sunusi labaran,  a Filin sauka da Tashin Jirage na Malam Aminu Kano dake Jihar Kano yayin da yake tsaka da Niyyar shiga Jirgi Dauke da da Jakunkuna biyu makare da Katin Cirar kudi wanda akafi sani da ATM zuwa Kasar Dubai.

Babban Kwantirolan hukumar Rashen Jihar Kano da Jigawa Nasir Ahmad , Shi ne ya bayanna hakan Jim kadan da mika Wanda ake zargin ga Hukumar Dake yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa Reshen Jihar Kano EFCC.

Nasir Ahmad ya bayyana cewa Hukumar ta kwastam ba za ta gajiyaba wajen Ganin ta Dakume Dukkanin Wasu masu Karya Doka ta Shige da Fice da kayayyakin da Aka Haramta ba.

Inda yace Matashin An kama shi ne da kimanin Katin cirar Kudi da Adadinsu yakai guda 5382 tare da Memory card guda biyu.

Da yake nasa Jawabin a yayin da Hukumar Hana fasa Kaurin ke Damka Wanda ake zargi ga Hukumar tashi ta EFCC,  Malam Sunusi Aliyu Wanda ke a Matsayin Shugaba Reshen Jihar Kano da Kuma Jigawa ya ce Tabbas Hukumarsu Ta na Mika Godiya ga Hukumar Hana Fasa Kaurin Bisa Jajircewarsu a bangaren Kame Duk wani Da Ake zargi da Laifi a Jihar.

Sunusi Aliyu yakuma Kara da cewa Za su zurfafa Bincike kan Wanda Aka Kama da wadannan ATM din dan Gano Gaskiyar Al’amarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here