Gwamnatin Jihar Jigawa Za ta Kafa Kwamitin Kar ta Kwana Don Tallafawa Wadanda Ambaliyar Ruwa Ya Shafa

0
123

Gwamnatin Jihar Jigawa ta kudiri Aniyar samar da Kwamitin Kar ta kwana Dan Ganin ta Rage Radadi ga wadanda Ambaliyar Ruwa ya Shafa musamman Manoman Shinkafa a Jihar.

Gwamman Jihar Abubakar Badaru Talamiz Shi ne ya bayyana hakan ta bakin Mai taimaka masa na Musamman kan fannun Noman Shinkafa a Jihar, Hon Jamilu Muhammad Dan Malam,  yayin da yake Ganawa da Manema labarai a Offishinsa.

Dan Malam ya bayyana cewa ya zuwa yanzu Gwamnatin Jihar ta Kammala shirye-Shiryen Bada Tallafin kayyayakin Noma ga shiyoyi Hudu da Abin ya Fi Kamari a Jihar,
Ciki kuwa har da Birnin Kudu,Gumel,Hadeja da kuma Kazaure wadanda sun tafka asarar da bazata iya Misaltuwaba,  har sai malaman Gona sun Kammala Bincike akai.

Shima ana sa bangaren Mataimaki na Musamman ga  Gwamnan Jihar,  ya Jigawa Hon. Dawaki ya ce Gwamtin ta jihar Jigawa ta samar da Iri kala Daban -Daban na zamani ga Manoman da Suka samu asarar Dukiya musamman Ma a fannin Noman Gero, Dawa,Madara, Shinkafa da dai sauransu.

Ka zalika Mataimaka ga gwamnan Sun ce Kamata yayi ace Matasa da sauran Al’umma sun Maida Hankali wajen Yin Noma Domin Dogaro da Kansu Dan Amfanuwar goben su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here