‘Yar Nuhu Ribadu ta yi Nadamar Bayyanar Hotunan ta a shafukan Sadarwa

0
153

‘Yar tsohon shugaban hukumar EFCC, Fatimah Ribadu wacce ta Auri dan tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ta wallafa a shafin ta na sadarwa na zamani a jiya Litinin inda ta ce ta na nadamar hotunan da suka bayyana a shafukan sadarwar na zamani.

Fatima Ribadu wacce ta Auri Aliyu Abubakar Atiku, a ranar Asabar an ga hotunan ta wadanda suke nuna surar jikin ta abin da ya sabawa koyarwar addinin musulunci.

“Nayi aure a ranar Asabar, 3 ga wata, wasu hotuna na da aka dauka a cikin gida sun fita har ana yada su a kafafen sadarwa”.

‘Yar Ribadu, ta kuma yabawa masu yi mata fatan Alkhairi bisa tsayawa wajen kare ta yayin da masu amfani da shafukan sadarwa suke sukar ta, duk da gaskiya suke fada mata.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here