Naira Marley Ya Janye Batun Yin Zanga-Zangar Adawa da Rundunar SARS

0
178

Shahararen mawakin nan, Naira Marley, ya yi mi’ara koma baya kan yunkurin sa na shirya zanga-zanagar lumana kan cin zarafin da ake zargin jami’an ‘yan sanda suna yi.

Mawakin ya wallafa a shafin sa na Twitter cewa ya dakatar da yin zanga-zangar ne saboda “an samu sauye-sauye da dama zuwa yanzu”.

“Baza mu yi zanga-zanga ba saboda an samu sauye-sauye da dama zuwa yanzu. A matsayin mu na Marlian za mu basu mako daya don ganin chanje-chanjen idan muka ga ba a sauya ba za mu shirya gagarumar zanga-zanga”, inji shi.

Ita ma rundunar ‘yan sanda ta kasa ta sanar a shafin ta na Twitter cewa, mai magana da yawun rundunar, DCP Frank Mba, zai yi tattaunawa kai tsaye da Naira Marley a shafun sadarwa na Instagram don amsa tambayoyi tare da tattaunawa kan damuwar matasan Najeriya kan ayyukan rundunar SARS.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here