Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta Soke Dakatarwar da aka yiwa Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso

0
108

Majalisar dokokin jihar Kano ta soke batun dakatarwar da aka yiwa shugaban karamar hukumar Kumbotso, Alhaji Kabiru Ado Panshekara.

A wata wasika da sakataren kwamitin majalisar kan kananan hukumomi, Lawan Yusuf Sagagi ya rubutawa majalisar karamar hukumar Kumbotso majalisar dokokin ta dakatar da Kansiloli 7 na karamar hukumar bisa sabawa dokar kundin tsarin mulki kamar yadda yake dauke a sashi na 55(1) na dokar jihar Kano ta shekarar 2006 tare kuma da sabawa majalisar dokokin jihar.

Wadanda aka dakatar din sun hada da Yusuf Ibrahim Kumbotso, Aminu Sani Panshekara, Najiyu Magaji Liman Danbare da Lawan Umar Mariri.

Ragowar sun hadar da Hamza Abdulkarom, Aimu Haruna da Magaji Alasan.

Idan za’a iya tunawa dai, Kansiloli 7 na karamar hukumar sun dakatar da shugaban karamar hukumar, Alhaji Kabiru Ado Panshekara bisa zargin badakala da dukiyar karamar hukumar da ta kai Naira Miliyan 177.

Haka kuma Kansilolin sun amince mataimakin shugaban karamar hukumar, Alhaji Sagir AbdulKadir ya ci gaba da jan ragamar karamar hukumar kafin kammala bincike.

Majalisar dokokin jihar a wasikar ta yi nuni da cewa dakatarwar ta fara aiki daga ranar 2 ga watan Oktoba zuwa 2 ga watan Janairu na shekarar 2021.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here