Ku Ajiye Aikin Koyarwa Ku Koma Noma, Gwamnatin Tarayya Ga Kungiyar ASUU

0
383

Karamin Ministan Ilimi, Mista Chukwuemeka Nwajiuba ya bukaci kungiyar Malaman jami’i’o ta ASUU, da su bar fannin koyarwa su koma yin noma, inda ya yi bayanin cewa ana bukatar karin manoma a kasarnan.

Haka kuma, a shirye-shiryen bude makarantu, Nwajuiba ya ce wasu daga cikin dabarun da aka sanya na hana yaduwar cutar COVID-19 za su hada har da ajin yamma domin dakile cunkosan jama’a.

Nwajuiba wanda ya kasance a matsayin bako cikin shirin gidan Talabijin na ARISE NEWS Channel a dake Abuja a jiya, ya bayyyana cewa dole ne dukkan makarantu su bi matakan kariya daga cutar COVID-19.

Ya ce “wasu mutanen watakil baza su yarda da abinda muke yi ba amma dole ne mu ci gaba da yin hakan. Dole ne ka ci gaba da bin matakan da aka sanya. Bama damuwa kan cewa an gamsu ko ta yaya aka gamsu ku yi tunani ‘ya yan ku su sanya safar rufe hanci da baki. Farko dai abi doka. Idan muka gano ba’a bin wannan doka, zamu hukunta wanda yaki bi”.

A batun yajin aikin kungiyar malaman jami’i’o ta ASUU kuwa ministan ya ce kungiyar tun da farko bata shiga yajin aiki kan annobar corona ba, sannan ya ce yakamata malaman makarantun su nemi sana’ar noma domin ana bukatar karin manoma a kasarnan.

Ya ce gwamnatin tarayya ta nuna kulawa da bukatun su.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here