Zaben Ondo:KwanKwaso Ya Jagoranci Gangamin Yakin Neman Zabe

0
166

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a jiya Lahadi ya jagoranci dubban magoya bayan jami’iyyar PDP wajen yakin Neman zaben kujerarar gwamnan jihar Ondo da za’a gudanar ranar 10 ga watan Oktoba da muke ciki.

Gangamin yakin neman zaben ya gudana ne a garin Ore, karamar hukumar Odigbo na jihar inda dubban magoya bayan jami’iyyar Dauke da jar hula suka bayyana sha’awar su ta zabar Eyitayo Jegede na PDP a ranar 10 ga watan Oktoba.

Rabi’u Musa Kwankwaso dai ya na daga cikin tawagar yakin neman zaben jami’iyyar PDP a zaben na Ondo.

A wani faifan Bidiyo da Kwankwaso ya wallafa a shafin sa na Twitter, an ga dubban magoya baya na shewa da kirarin jami’iyyar.

Za dai a gudanar da zaben jihar Ondo ne a ranar 10 ga watan nan na Oktoba inda za’a gwabza tsakanin yan takara 17 ciki har da gwamnan jihar mai ci Rotimi Akeredolu na APC, Agboola Ajayi na ZLP da Eyitayo Jegede na PDP.

Kwankwaso dai ya yi irin wannan gangami a zaben gwamnan jihar Edo wanda Gwamna Obaseki na PDP ya samu nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here