Yanzu-Yanzu: Shugaban Amurka Donald Trump Ya Warke daga Cutar korona

0
108

Shugaban kasar Amurka, Donal Trump ya warke daga cutar COVID-19.

Ya yi bayanin cewa yana jin kwarin jiki “fiye da yadda nake ji a shekaru 20 da suka gabata”.

Shugaban dai ya kamu da cutar COVID-19 a ranar Juma’a tare da matar sa kuma aka kwantar da su a Asibiti tun lokacin.

Trunp, wanda yake neman a sake zaben sa a karo na biyu ya ce zai bar cibiyar lafiya ta Walter Reed Medical inda yake jinya daga yanzu zuwa kowanne lokaci.

Ya wallafa a shafin sa na Twitter cewa” Zan bar cibiyar Walter Reed yau da karfe 6:30 na dare. Ina jin sauki! Kar ku ji tsoron COVID.”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here