Yanzu-Yanzu: Mai Magana da Yawun Donal Trump Ta Kamu da Cutar COVID-19

0
89

Kayleigh McEnany, Sakatariyar Yada labaran fadar White House ta kamu da cutar COVID-19.

Ta kamu da cutar ne kwanaki uku bayan an kwantar da shugaban kasar, Donal Trump wanda shi ma ya kamu da cutar ta Corona.

McEnany a wata sanarwa da ta fitar yau Litinin ta ce, “Bayan gwaji da dama ban kamu da cutar ba wanda kulluma ana yi har da na baya-bayan nan ranar Alhamis, a saifiyar yau Litinin dai gwaji ya nuna na kamu da cutar COVID-19.

“Ba wani Mai daukar rahoto, Mai fitar da labarai ko mamba na yan jarida da aka lissafa shi a tsarin wadanda aka yi mu’ammala ta kusa”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here