
Tshohon shugaban Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, Farfesa Abdulhamid Isa Dutse ya rasu.
Jaridar PRIME TIME NEWS ta samu labarin rasuwar sa a yau Litinin.
Har zuwa rasuwar, Farfesa Dutse ya yi aiko a sashin likitanci, Asibitin kwararru na Riyadh dake kasar Saudiya.
Tsohon shugaban asibitin ya gudanar da bincike da dama a fannin cutar mai karya garkuwar jiki da rigakafin cutuka masu yaduwa.
Ya kuma wallafa makaloli tare da halartar taruka na kasa da kuma kasashen duniya.