Rashin Tsaron Zamfara: Iyalan Al-kalin Da Aka Yi Garkuwa Da Shi Za Su Sayar Da Gidansu Domin Fansar Sa – Bincike

0
152

A ranar 11 ga watan Satumba na shekarar 2020, babban limamin masallacin juma’a na Umar Bin Khaddabi dake Jihar Zamfara, Shekh Umar Kanoma ya yi kukan cewa an yi garkuwa da alkalan kotun shari’a guda biya, Malam Sabiu Abdullahi da Malam Shafi’i Jangebe a jihar.

Sheikh Kanoma wanda ya yi magana yayin gabatar da hudubar Sallar juma’a inda ya bukaci gwamna Matawalle ya tabbatar da an kubutar da alkalan guda biyu.

Jaridar PRIME TIME NEWS ta rawaito cewa a ranar 12 ga watan Satumba, alkalan guda biyu suna kan hanyar su ta dawowa daga Nijar yayin da al’amarin ya faru.

An rawaito cewa alkalan guda biyu sun halarci taron wa’azi ne a Maradi ta kasar Nijar.

“Yayin da muke bukatar addu’a daga al’umma don kubutar alkalan biyu, yana da muhimmanci ayi kira ga Gwamna Matawalle ya yi duk mai yuwuwa don ganin an kubutar da su tare da dawo da su cikin iyalan su”.

Wata majiya da ta nemi a boye sunanta ta shaidawa PRIME TIME NEWS cewa, iyalan daya daga cikin iyalan alkalin suna fafutukar siyar da gidan su don ceton alkalin.

Majiyar ta tabbatar da cewa daya daga cikin alkalan da aka yi garkuwa da su ya umarci iyalan sa da su siyar da dukkan kadarorin sa kuma su nemi tallafi daga mutane tunda gwamnatin jihar ta ki ceto su.

“Wasu daga cikin iyalan alkalin da aka sace sun fara bayyana bukatar neman tallafi a shafukan sadarwa na zamani daga mutane”.

Yanzu dai kusan kwanaki 25 da yin garkuwa da alkalan, sai dai wata majiya ta ce har yanzu ba wani yunkuri da ake domin ceto su.

Liman Umar Kanoma yayin hudubar ya yi kira ga yan bindiga da sauran masu aikata laifi da su tuba su nemi gafarar Allah.

Babban Limamin ya kuma yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su tabbatar da sun sauke nauyin dake kan su wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here