Ganduje Ya Amince da Nadin Barista Salisu a Matsayin Sakataren Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano

0
116

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadin Barista Salisu Muhammad Tahir a matsayin Sabon Sakatare kuma mai bada shawara ga hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano.

Nadin ya biyo bayan shawarar da shugaban hukumar, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ya bayar a wata wasika ga gwamnnan.

Barista Salisu Tahir ya maye gurbin tsohon sakataren Barista Rabi Ibrahim Waya wacce aka mayar da ita ma’aikatar shari’a ta jihar.

A takardar da Muhuyi Magaji ya aikawa gwamnan ya ce bukatar nadin yana kan tsarin sashi na 10 na dokar hukumar sannan Barista Salisu M Tahir ya cika dukkan wasu matakan doka.

Barista Salisu M. Tahir dai shine Daraktan karbar korafe-korafe da sasantawa na hukumar kafin nadin nasa.

Barista Salisu M Tahir lauyan gwamnati ne da yake da kwarewar aiki ta shekara 18.

Haka kuma an nada Barista Zakiyya Haruna a matsayin magatakardar sabuwar makarantar yaki da cin hanci da rashawa da aka kafa a jihar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here