An Karamma Ma’aikatan Hukumar Dake Kula da Filaye ta Jihar Kano

0
93

Babbar Sakatariya a hukumar kula da filaye ta jihar Kano, Dr. Zainab Ibrahim Braji ta mika shedar girmamawa ga ma’aikata 15 na hukumar ciki har da Darakta da mataimakin darakta.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Murtala Shehu Umar ya fitar a yau Litinin ta ambato babbar sakatariyar yayin da take jawabi bayan gabatar da lambar yabon na cewa, ta ji matukar dadin yadda matasan ma’aikatan suke nuna kwarewar su tare da gudanar da ayyukan su yadda yakamata.

Ta yi nuni da cewa wadanda aka karrama din an zabe su ne bisa kokarin su da kwazon su.

Dr Braji ta yi bayanin cewa duk wanda ya aikata mai kyau za’a karrama shi, wanda kuma suka yi sabanin haka za’a hukun ta su kamar yadda dokar ma’aikata ta tanada.

Sanarwar ta kara da cewa , idan za’a iya tunawa dai babbar Sakatariyar ta karrama ma’aikata 4 a watan Maris na shekarar 2020, a matsayin na farko inda ta yi alkawarin ci gaba da yin hakan.

Wadanda aka karrama din sun hada da Babban Surveyor na Kano, Dayyabu Dandikko Rogo a matsayin babban Darakta mafi kwazo da Nasiru Ibrahim Mariri a matsayin gwarzon mataimakin darakta.

Sashin bincike da tantancewa na hukumar, shine sashin da yafi kowanne kokari sai sauran mutane 13 daga sashi daban-daban da aka karrama kamar yadda sanarwar ta bayyana.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here