Kwalejin Fasaha Ta Kwara Za ta Hukunta Duk Daliban Da Aka Kama Suna Sumbata ko Rungumar Juna a Makarantar

0
134

Hukumomin kwalejin fasaha ta jihar Kwara dake Ilorin sun ce Kwalejin za ta kori duk dalibin da aka kama yana kin bin ka’idojin kariya daga cutar COVID-19 a makarantar ciki har da Sumbata, Runguma ko gaisawar hannu.

Makarantar ta hanyar kwamitin kwararru na yaki da cutar COVID-19 na makarantar ta sanya matakan yin hukunci ga duk dalibi ko ma’aikacin kwalejin da ya sabawa matakan kariyar a harabar makarantar.

A wani rubutun sanarwa da makarantar ta fitar wanda kuma Lakcara a kwalejin, Taiwo Hassan ya tabbatarwa da Jaridar THECABLE makarantar ta yi bayanin cewa za ta dauki tsarin ”Ba wanda zai shiga Kwalejin sai da Safar rufe baki da Hanci”.

Cikin matakan da aka sanya shine, duk wanda yaki sanya takunkumin rufe hanci da baki, kin bada tazara, gaisawar hannu, runguma da Sumbata za’a dakatar da shi Zangon karatu daya wato Semester daya.

Sannan ta ce za’a iya dakatar da dalibi a gabadaya zangon karatu idan ya aikata rashin bin doka.

Ga ma’aikatan da suka gaza sanya takunkumin rufe fuska, kin bada tazara ko gaisawa, za’a ci tarar su Naira Dubu 1 sannan za a basu wasikar gargadi.

Matakan da Kwalejin ta ke dauka suna zuwa ne a yayin da ake shirin komawa makaranta a ranar 12 ga watan Oktoba kamar yadda gwamnatin tarayya ta bada dama.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here