Kananun Yara Masu Bara sun Yawaita a Titunan Jahar Kano.

0
185

 

Tun bayan da gwamnatin jahar Kano ta soke yin bara a fadin jahar, wata sabuwar dabi’a ce ta bayyana na yara masu bara ,inda suka yawaita a manya tituna dake cikin birnin jahar bisa rokan a basu kudi domin su ciyar da kansu ko kuma yi wa kansu wata bukatar.

Galiban yaran da suka dauki wanna dabi’ar basa wuce shekara (8 zuwa 15).

Hakazalika,Yaran masu bara sunfi rokon wadanda suke cikin manya motoci ko na cikin motar haya,har da masu tafiya a kasa mussaman idan suka duba shigar da mutum ya yi.

A wata hira da jaridar PRIME TIME HAUSA tayi da yaran da ta gani suna bara a titi Ahmad Musa Hotoro da misalin karfe 8:30 na dare cikin walwala ba tare da tsoron mai zai faru dasu ba sun bayyana dalilan da yasa suke bara .

“Muna bara ne sabida bamu da kudi da zamu tada jari kasuwanci,shine muke rokon wadanda suka fi iyayen mu kudi da su taimaka mana,duk da cewa da yawan mu da sanin iyayen mu muke yin bara domin wani zubi da kudi ake cin abinci a gida,kuma muna fitowa da safe da kuma magariba ,lokacin an fi samu kudi da ya haura dubu 2 ko kasa da haka,sau tari muna gudu daga makaranta domin mu zo mu fara bara ba tare da sani iyaye mu ba ko malamai.

Jaridar PRIME TIME HAUSA dai tayi nazari tituna da ake samu yawan yara masu bara kamar titi gidan gwamna,Na’ibawa Zaria Road,Kabuga,Gadar lado,zoo Road,sultan road,Dan Agudi,titi nan kasuwa, asibitoci da makamansu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here