Hukumar kula da aikin Hajj ta Kasa Ta Kaddamar da Adashin Gata na Hajji a Kano

0
88

Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa(NAHCON), ta kaddamar da tsarin fara adashin kudin tafiya aikin hajji a Kano.

Hukumar kula da aikin hajji ta kasa ce dai ta bullo da shirin don baiwa musulmai a Najeriya damar gudanar da aikin Hajji ko da sau daya ne a rayuwar su.

Yayin da yake jawabi wajen taron, wanda aka gudanar da shi a sansanin Alhazai na Kano(Hajj Camp) yau Lahadi, Babban jami’in hukumar ta NAHCON, Barista Zikirullah Kunle Hassan ya bayyana farin ciki kan yadda shirin ke gudana.

Ya ce, an dauTsawon shekaru goma wajen ganin tabbatuwar shirin har zuwa yau da ya cimma nasarori.

Sannan ya kara da cewa, shirin na samun goyan bayan sashi na 7 na dokar da ta kafa hukumar wanda ya ce ita ta bawa hukumar damar yin irin wadandan tsare-tsare dama wasu, “Samarwa, lura da tafikar da tsarin ajiyar kudi kadan-kadan don yin aikin Hajji zai kasance ne karkashin kulawar hukumomin jin dadin alhazai na jihohi”.

Hassan ya kuma yi bayanin cewa, tsarin shine irin sa na farko a yankin Afrika, a sanin sa babu wani tsari kamar haka.

Haka kuma, ya taya murna ga hukumar gudanarwa da ma’aikatan hukumar ta NAHCON, musamman wadanda ke a bangaren shirin bisa kokarin su don tabbatar da abin da ya kira da “tsarin gaskiya mafi rinjaye”.

“Tun kaddamar da mu a watan Fabarairu na shekarar 2020, hukuma ta ta sanar da niyyar ta ta chanza tsarin tafiya aikin Hajj, musamman wajen tattara kudi, don saukakawa ga mutanen mu, abin da muka yi niyyar yi shine abinda muka taru a yau muna shedawa”.

Shugaban ya kuma ce taron, cika alkawari ne na hukumar da suka yi amfani da bankin Ja’iza Bank wajen farawa.

Shima ana sa jawabin, Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana farin cikin sa bisa samar da shirin tare da zabar Kano ta zama wajen kaddamar da shirin.

Ganduje ya ce, ansan jihar da himma wajen al’amarun aikin Hajji, inda ya kara da cewa ya bada umarni ga hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Kano da ra fara shirye-shiryen aikin hajji na shekarar 2021.

Ganduje ya kuma bada shawara ga dukkan ma’aikatan jihar da su shiga cikin shirin, wanda ya bayyana a matsayin kasaitacciyar Dama ga kowa wajen yin aikin Hajji wanda daya ne daga cikin rukunonin addinin musulunci.

“Muna kira ga ma’aikata da su shiga cikin shirin. da kadan-kadan, wata rana ma’aikaci zai tara kudin da zai je aikin Hajj.

“Mun kuma dauki addinin musulunci da muhimmanci shi yasa muka kafa ma’aikatar kula da harkokin addinin musulunci”, Inji Ganduje.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here