‘Yan Daba Sun Kai Hari Kan Masu Ababen Hawa a Kano

0
276

Wasu yan daba sun kai hari kan masu ababan hawa a Junction din Kofar Dan’agundi dake birnin Kano lamarin da ya haifar da fargaba kamar yadda wani wanda lamarin ya faru a kan idon sa ya bayyana.

Mutumin mai suna Lawan Musa ya shaidawa jaridar Newstunnel cewa wasu bata gari dauke da makamai sun farwa masu ababan hawa suna kwace wayoyin su.

“Sun sace wayoyi kuma sun jiwa wasu rauni”, inji shi.

Yayin da aka tuntubi, kakakin rundunar yan sanda ta jihar Kano, DSP Abdullahi Kiyawa kan batun ya ce har yanzu ba su tabbatar da faruwar lamarin ba sannan ya yi kira ga al’umma su kai rahotan duk wani mai aikata laifi ga rundunar yan sanda.

A yan kwanakin nan dai ana samun yawaitar masu kwacen waya a jihar ta Kano.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here