Wata Mata ta Yanka ‘ya’yanta Biyu a Kano

0
719

An zargin cewa wata mata mai suna Hauwa ta yanka ‘ya’yan ta guda biyu a Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa matar ta kashe su ne yayin da mijinta, Ibrahim Haruna ya kara aure.

Matar wacce take zaune a unguwar Diso dake karamar hukumar Gwale, ana zargin ta kashe dan ta mai suna Yusif, Dan shekara 5 da yar uwarsa, Zahra’u mai shekaru 3.

Malam Ahmad Bello, mai unguwar Diso ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya yi Allah wadai da aikin.

Rahotanni sun bayyana cewa Baban yaran ba ya gari yayin da lamarin ya faru.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here