Wani Gini Da ake Zargin Mara Inganci ne Ya Rushe tare da jawo Asarar Rai a Kasuwar Kurmi dake Kano

0
170

Wani gini da ake zargin anyi shi ba inganci ya rufta kan mutane a kasuwar Kurmi dake karamar hukumar Birni a Jihar Kano inda wata mata ta rasa ran ta yayin da wasu suka jikkata.

Ginin mai hawa daya dake ‘Yan mota a kasuwar Kurmi ya rushe ne da yammacin yau Asabar inda ya rufta kan mutane hudu.

Wani wanda abin ya faru a kan idon sa wanda kuma ya nemi a sakaya sunan sa yace tun farkon fara ginin makotan mutumin dake aikin gina shagon suke bashi shawara kan cewa ya chanza ginin saboda rashin ingancin sa.

“An bashi shawara kan ya gyara, amma yaki sai ya dinga takamar cewa ya samu amincewar gina wajen daga hukumomin karamar hukumar ta birni,

“Dazu bayan Sallar Azahar ginin ya fado kan mutane hudu maza da mata ciki har da mai goyo” inji mutumin.

Shima ana sa bangaren, kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saidu….. ya tabbatar da faruwar lamarin a tattaunawa ta wayar Tarho da ya yi da jaridar PRIME TIME NEWS.

“Mun Samu Kira da Misalin karfe 2:50 na rana daga wani bawan Allah mai suna Jazuli Abubakar daga ita wannan Kasuwa ta Kurmi, jami’an mu sun isa wajen kuma sun tarar da gini ne hawa daya ya rushe kuma ya rufe mutum hudu a ciki, an yi nasarar ceto mutum 3 a raye akwai mace daya da an kai ta asibitin Murtala an tabbatar da ta rasu”.

Dangane da batun zargin da ake yi na cewa anyi ginin ba bisa ka’ida ba kuma ba shi da inganci, kakakin hukumar ya ce suna kan bincike kan lamarin.

Yayin da wasu ke alaqanta faduwar ginin da gine-gine ba bisa ka’ida ba da ake zargin hukumomin kasuwar da bada izinin yin sa tare da hadin gwiwar mahukunta a karamar hukumar Birni ta jihar Kano, wasu na ganin mamakon ruwan sama da aka yini ana yi yau a jihar Kano ne ya haifar faduwar ginin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here