Shugaban Kwalejin Fasaha ta Auchi Ya Rasu

0
128

Shugaban Kwalejin Fasaha ta Auchi dake jihar Edo, Dr. Momodu Sanusi Jima ya rasu.

Ya rasu ne a daren jiya Juma’a.

Jami’in hulda da jama’a na kwalejin, Mista Mustapha Oshiobugie, ya ce Jimah ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya.

“Zan iya tabbatar wa cewa ya rasu, za’a binne gawar sa yau Asabar da karfe 10 na safe kamar yadda addinin musulunci ya tanadar”, inji Oshiobugie.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here