Oshiomhole Ya na Bayar Da Miliyan Dubu 1 ga duk Jihar Da APC Ke son Samun Nasara -Wambai

0
123

Ahmed Wambai, tsohon mataimakin shugaban jami’iyyar APC na shiyyar Arewa ta Tsakiya ya ce dakataccen shugaban jami’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya bayar da kudi miliyan dubu 1 ga dukkan jihar da jami’iyyar ta ke son samun nasara.

Wambai ya bayyana Oshiomhole a matsayin shugaban dake son samun nasarar jami’iyyar. Amma ya ce wasu daga cikin gwamnonin APC sun taru wajen yin waje da shi daga ofis.

A wata tattaunawa da jaridar THE SUN, Wambai ya ce Oshiomhole a matsayin shugaban jami’iyyar bai taba karbar kudi daga gwamnoni ba don tafikar da jami’iyyar, maimakon hakan ya na taimakawa jami’iyyar wajen samun kudin shiga.

“A tarihi jami’iyyun siyasa , Oshiomhole ya kasance shugaban jami’iyya da gwamnoni basa bashi kudi , ba wani gwamna da ya taba bayar da gudunmawa wajen tafiyar da jami’iyyar a karkashin Oshiomhole. Mun yi hakan ne don jami’iyyar ta zama mai zaman kanta”, ini shi.

“Bamu taba cire hula mun je wata ma’aikata don neman kwangila ba domin tafiyar da jami’iyya. Oshiomhole ne kadai mutumin da yake bada miliyan 20 da miliyan 10 ga yan takarar Sanatoci da yan majalisa yayin zabe.

“Shine kadai mutumin da ya ba wa wasu yan takarar gwamnoni a jihohin da muke son samun nasara kamar Imo, Kwara, Gombe da Zamfara Naira Miliyan dubu 1 kowacce, jihar Benue kuma miliyan 700. Mun yi hakanne duk daga aljihun jami’iyyar. A tarihin jami’iyyun siyasa ba wanda ya taba haka. Tambaye ni a ina muka samu kudin, an same su ne ta hanyar siyar da form din yan takara” inji shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here