Kwankwaso, Ganduje da El’Rufai Sun Halarci Daurin Auren Dan Gidan Atiku

0
200

Jagoran jami’iyyar APC na Kasa, Bola Ahamd Tinubu, Gwamanan jihar Yobe, Mai Mala Buni, da Bisi Akande a yau Asabar sun halarci daurin auren ya’yan Atiku Abubakar da tsohon shugaban hukumar EFCC, Malam Nuhu Ribadu a Abuja.

Haka kuma shugabannin siyasa daga jami’iyyar APC da PDP gami da yan kasuwa sun halarci bikin.

Andai daura Auren ne tsakanin Aliyu Abubakar Atiku da Fatima Ribadu a birnin Abuja.

Atiku, wanda shine Wazirin Adamawa, dan jami’iyyar PDP ne yayin da Ribadu yake jami’iyyar APC.

Haka kuma an ga manyan siyasa dake hamayya da juna kamar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Dr. Abdullahi Umar Ganduje a wajen Daurin Auren.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here