Gawuna Ya yi Kira Ga Al’ummar Musulmai Da Su yi Riqo da Koyarwar Addinin Musulunci

0
197

Mataimakin Gwamnan jihar Kano, Dr. Nasiru Yusif Gawuna ya yi kira ga al’ummar musulmi da su dinga koyi da kyawawan halaye da addinin musulunci ya koyar, inda ya bayyana hakan a matsayin babbar hanyar kawo mafita ga matsalolin da al’umma suke fuskanta.

Gawuna ya yi bayanin cewa ” ta hanyar neman ilimin addinin tare da aiki da abinda muka koya, tabbas zamu magance matsalolin dake damun al’umma a kasarnan”.

Mataimakin gwamnan ya yi kiran ne a yau Asabar yayin da yake jawabi a taron Mauludin Shekh Ahamad Tijjani wanda magoya bayan darikar tijjaniyya suke gabatarwa a massalacin Garba AD dake unguwar Jakara, a karamar hukumar Birnin Kano.

A cikin wata sanarwa da Sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan, Hassan Musa Fagee ya fitar ta ambato Gawuna na cewa addu’ar da musulmai suke yi a jihar na neman dauki da kariyar Allah ita ce babban dalilan da yasa Kano ta ke zaune lafiya tsawon lokaci, inda ya kara da cewa magoya bayan Tijjaniya sun taka rawa sosai akan hakan.

“Muna fuskantar matsalar tsaro wanda ke kawo tsaiko ga ci gaban yankin arewacin Najeriya, insha Allah hakan na zama tarihi sannan muna samun kariya daga Allah ta hanyar addu’o’i”.

Gawuna ya kuma nuna farin cikin sa ga wadanda suka shirya taron tare da tabbatar musu cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafawa harkokin addini.

A nasa jawabin, Khalifan Shekh Sani Kafinga, Sheikh Farouk Hassan Kafinga ya ce ana shirya Mauludin ne duk shekara don bayyana rayuwa gami da koyar Shekh Ahmad Tijjani tare da hada kan mabiya darikar Tijjaniya a kasa baki daya.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here