Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Umarnin Komawa Makarantun ‘Unity Schools’

0
147

Gwamnatin tarayya ta bada umarni ga makarantun Sakandire na Unity School wadanda aka rufe sakamakon cutar Corona da su koma karatu ranar 12 ga watan Oktoba da muke ciki.

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ne ya sanar da bude makarantun a yau juma’a a Abuja.

Ministan ya ce, makarantu a fadin kasar nan suna tattaunawa don fitar da ranar da za’a dawo karatu tare da tabbatar da akwai matakan kariya yayin da aka koma makarantun.

Adamu Adamu ya kuma yi gargadin cewa, makarantun da suka gaza bin ka’idojin kariya daga cutar COVID-19, za’a rufe su idan aka samu bullar cutar a makarantun.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here