Wani Matashi Mai Shekaru 22, Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Wani Tafki a Kano

0
154

Mazauna karamar hukumar Ungogo dake jihar Kano sun ce wani matashi dan shekara 22 ya nitse a wani tafki a yammacin yau juma’a bayan ya fada ciki.

Da misalin karfe 2:30 na rana jaridar PRIME TIME NEWS ta samu rahotan fadawar matashin daga wata majiya.

Matashin mai suna Khalifa ya fada tafkin ne bayan mutane sun tafi Sallar Juma’a Kuma gawar ta sa bata fito ba sai da jama’ar garin suka fito da ita.

Sannan rahotannin sun bayyana cewa ba’a ga tawagar ceto a wajen da abun ya faru ba yayin da matashin ya fada ruwan da misalin karfe 4 na yamma.

“Mutanen dake yankin ne suka fito da gawar matashin daga tafkin da misalin karfe 4 na yamma” inji wata majiya.

“An fito da gawar mutumin daga tafkin da karfe 4 na yamma tare da taimakon mazauna yankin”, inji majiyar.

Mutanen karamar hukumar ungogo dai suna amfani da tafkin wajen hako yashi don yin gine-gine.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here