Shugaban Kasar Amurka Donald Trump Ya Kamu da Cutar korona

0
121

Shugagaban Kasar Amurka, Donal Trump ya ce shi da matar sa Melania Trump sun kamu da cutar COVID-19, yanzu haka suna killace.

Shugaban kasar mai shekaru 74, wanda kuma yake cikin rukunin mafiya hatsari, ya sanar da labarin ne a shafin sa na Twitter.”zamu samu sauki tare” ya rubuta.

Hakan na zuwa ne bayan daya daga cikin masu taimaka masa ta kamu da cutar.

Hope Hicks, mai shekaru 31, mai baiwa shugaba Trump shawara na kusa ta kamu da cutar.

Sun yi tafiya tare da shi a jirgi daya a mahawarar yan takarar shugaban kasa da aka yi tare da shi da Joe Biden ranar Talata, wasu daga cikin dangin Mista Trump wadanda suka halarci mahawarar an gan su ba tare da takunkumin rufe hanci da baki ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here