Gwamnatin Jihar Kano Ta Amince Da Komawa Makarantu

0
171

Gwamnatin jihar Kano ta amince da sake bude makarantu a jihar bayan shafe tsawon watannin makarantu suna rufe sakamakon annobar COVID-19.

Gwamman jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne ya bada umarnin sake bude makarantun daga ranar 11 ga watan Oktoba a takardar neman sake bude makarantu da kwamishinan ilimi na jihar Kano, Malam Muhammad Sanusi Kiru ya gabatarwa gwamnan.

An amince da sake bude makarantun tare da sanya matakan da suka hada da :
a. Dukkan Makarantun islamiyya za su koma karatu tare da bin tsarin ka’idojin kariya daga cutar COVID-19 daga ranar 11 ga watan Oktoba.

b. Daliban makarantun aji na 6 na makarantun gwamnati da na masu zaman kan su za su koma ranar Litinin 11 ga watan Oktoba.

c. Yan aji 1 da 2 za su dinga halartar karatu a ranakun Litinin da Talata yayin da yan aji 3, 4 da aji 5 za su dinga zuwa makaranta a ranakun Laraba da Alhamis da juma’a daga ranar 11 ga watan Oktoba.

d. Yan aji 1 na karamar Sakandire da na babbar Sakandire a makarantun gwamnati da masu zaman kan su da na jeka ka dawo za su zauna a gida zuwa mako 5 har sai karshen jarrabawar Qualifying don tabbatar da bada tazara a ajujuwa da guraren kwanan dalibai.

e. Dukkan makarantun tsangaya na Almajirai za su koma karatu a ranar 11 ga watan Oktoba.

f. Yan ajin karamar sakandire aji na 2 da yan ajin 2 na babbar sakandire za su koma don yin shirin jarrabawar Qualifying .

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here