Bai Dace Najeriya Ta dinga Siyar da man fetir Kasa da Farashin da Saudiya Ta ke Siyarwa ba -Buhari

0
456

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya ce bai dace Najeriya ta siyar da man fetir kasa da yadda kasashe makota ke siyar da shi ba.

Ya bayyana hakan ne a safiyar yau Alhamis yayin da yake jawabin bikin cikar Najeriya shekaru 60 da samun yan’ cin kai a Abuja.

Buhari ya ce “yan uwana yan Najeriya, a bisa kari na matsalolin kiwon lafiyar al’umma na aikin da ake yi wajen hana yaduwar cutar Corona, mun fuskanci matsi na raguwar samun kudaden shiga daga kasar waje da kudaden shiga na gida bisa raguwar farashin man fetir da kashi 40 da raguwar harkokin kasuwanci, wanda ya kai ga raguwar kudin shiga da gwamnati ke samu da kashi 69″.

Buhari ya kara da cewa, ” Farashin man fetir a Najeriya an kara shi. Yanzu muna siyar dashi Naira 161 duk lita.

“Kasar Chadi, wacce take fitar da man fetir ta siyar da lita daya kan Naira 362. Nijar ita ma tana fitar da man fetir tana siyar da lita kan 346. Kasar Ghana ma wacce ke da albarkatun man fetir tana siyar da lita kan 326. Kasar Egypt ta na siyarwa 211 sai kasar Saudiya ta na siyarwa kan Naira 168 duk lita.

” Shirme ne ace man fetir yafi sauki a Nijeriya kan kasar Saudiya”.Inji Buhari.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here