Anyi Garkuwa da Shugaban Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna

0
113

Rahotannin sun bayyana cewa, anyi garkuwa da shugaban karamar hukumar Kaura, Katuka Humble dake jihar Kaduna.

Kamar yadda wata majiya ta bayyana, lamarin ya faru ne a ranar Lahadi yayin ake goye da shi kan babur a kan hanyar sa ta zuwa gidan gonar sa dake Kauyen Kiduni a karamar hukumar Chikun ta jihar.

Yan bindiga sun bude wuta kan babur din, inda suka kashe mai jan babur din kafin su sace shugaban karamar hukumar.

“An sace shugaban karamar hukumar a hanyar sa ta zuwa gona a ranar Lahadi. Gonar tana nan a kauyen Kiduni dake karamar hukumar Chikun. Yan bindingar sun harbe su tare da kashe matukin babur din da ya goya shugaban karamar hukumar sannan suka sace shi”, inji majiyar.

Yayin da aka tuntubi, Mohammed Jalige, kakakin rundunar yan’sanda ta jihar Kaduna, bai amsa kiran waya da sakon kar ta kwana da aka tura masa.

Mazauna yankunan jihar Kaduna dai na fama da matsalar garkuwa da mutane da kashe-kashe.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here