‘Yan Sanda Sun Kama Matashin Da Ya yada Bidiyon Lalata da Tsohuwar Budurwar sa a Sokoto

0
277

Rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Sokoto ta tabbatar da kama Baffa Tafida, wanda ake zargin da yada bidiyon da ake lalata da wata budurwa a kafafen sadarwa na zamani.

An yi zargin cewa anyi lalata da yarinyar ne a shekarar 2017, sai dai wanda ake zargin ya saki bidiyon makwannin kadan kafin Auren ta.

An fasa yin auren ne bayan yaduwar bidiyon.

Mai magana da yawun rundunar yan’sandan, ASP Muhammad Sadiq, ya tabbatarwa da manema labarai a jiya Talata cewa ana tsare da Baffa don zurfafa bincike kan lamarin.

Mahaifiyar yarinyar wacce aka boye sunan ta, tun da fari ta fadawa manema labarai cewa babban wanda ake zargin ya yi lalata da yar’ta a shekarar 2017 sanda take yar shekara 16.

Mahaifiyar yarinyar ta yi zargin cewa wanda ake zargin ya ajiye bidiyon tsawon shekaru uku da niyyar bata rayuwar yarinyar.

“Wanda ake zargin ya tura bidiyon ga wanda zai auri ya’ ta da sauran groups na Onlines”, inji ta.

Ta ce, an kammala shirin auren yar ta, wanda za’ayi ranar 17 ga watan Oktoba, yayin da Baffa ya saki bidiyon sa yana lalata da yarinyar.

Matar ta ce, lamarin ne yasa angon ya janye daga neman auren.

Haka kuma kamfanin dillacin labarai na kasa(NAN) ya rawaito cewa, Gwamna Aminu Tambuwal ta bakin mai magana da yawun sa, Muhammad Bello na bada umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here